Ankai wa Sansanin Sojin Amurka Hari a Bagadaza

 


An kai hari kan wani sansanin sojin Amurka dake kusa da filin tashi da saukar jiragen sama na Bagadaza, a cewar majiyoyin yada labarai da dama.


IRNA ta nakalto daga Kafofin yada labaran Iraqi cewa an ji karar fashewar wasu abubuwa guda hudu a kusa da sansanin Victoria bayan wani harin makami mara matuki ko makami mai linzami da safiyar Talata wanda kuma ya haifar da kararrawar sanarwa (Siren) a wurin.


Har yanzu dai ba a fitar da karin bayani kan wannan harin ba.


Kungiyoyin gwagwarmaya na Iraki sun sha kai hare-hare kan sansanonin Amurka da cibiyoyin da ke cikin kasar da ma makwabciyarta Syria a matsayin ramuwar gayya ga goyon bayan da Amurka ke baiwa gwamnatin sahyoniyawa na yakin kisan kare dangi da take yi a yankin.


A ranar Litinin ne kungiyar Islamic Resistance a Iraki, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, ta kai hari da makami mai linzami da jirage marasa matuka a yankunan da Isra'ila ta mamaye.


A ci gaba da tinkarar gwamnatin sahyoniyawan mamaya da kuma taimakon al'ummar Palastinu da Labanon, da kuma mayar da martani kan kisan kiyashin da ake yi wa fararen hula da suka hada da yara da mata da tsoffi, mayakan gwagwarmayar Musulunci na kasar Iraki sun kai farmaki kan wasu muhimman wurare guda hudu na Palasdinawa da ta mamaye, in ji sanarwar.


Daga cikin harin na ranar Litinin ankai hari da Jirage marasa matuka guda biyu zuwa Haifa, tare da kuma kai hari kan wata muhimmiyar manufa a tsakiyar yankunan Falasdinawa da aka mamaye.


A cikin mako da watanni da suka gabata, gwagwarmayar Iraki ta kai hari kan muhimman wurare a Eilat, dake kudancin Palasdinu da ta mamaye."

Post a Comment

Previous Post Next Post