'Yan Muqawama Dake Ƙasar Iraqi Sun kai Sabon Hari a "Isra'ila"

 


Kungiyar gwagwarmayar Islama a Iraki ta sanar da cewa ta kaddamar da sabbin hare-hare kan "Haramtacciyar Ƙasar Isra'ila" a yankunan Falasdinawa da ta mamaye a matsayin ramuwar gayya ga mummunan Yaƙin da Tel Aviv keyi kan Gaza da kuma hare-haren da ta kai ga Lebanon.


Kungiyar masu fafutuka ta Iraki ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a daren jiya Lahadi cewa ta kai hari kan wata muhimmiyar manufa a birnin "Eilat" mai tashar jiragen ruwa da aka mamaye ta hanyar amfani da jirage marasa matuka.


“A ci gaba da tunkarar 'yan mamaya, da kuma goyon bayan al’ummarmu a Palastinu da Lebanon, da kuma mayar da martani ga kisan kiyashin da ‘yan ta’addan suka yi wa fararen hula da suka hada da yara, mata da tsofaffi, mayakan Gwagwarmayar Islama a Iraki a yau Lahadi 29-09-2024, sun kai hari kan wata muhimmiyar manufa a Umm al-Rashrash [Eilat] a cikin yankunanmu da aka mamaye, ta hanyar amfani da jirage marasa matuka," in ji sanarwar.


Kungiyar ta kara da cewa wata tawagar jirage marasa matuka ta kuma kai hari kan wasu wurare biyu a yankunan da ta mamaye.


Dakarun Islama na Iraki sun ce farmakin na uku ya kai hari kan wuraren "Isra'ila" da makamai masu linzami.


Kungiyar ta jaddada cewa, za ta ci gaba da gudanar da ayyukan ta na yaki da "Isra'ila" domin goyon bayan Falasdinawa a Gaza da Lebanon.


Har ila yau a safiyar Lahadi, mayakan kungiyoyin gwagwarmaya na Iraki sun kuma kaddamar da hare-haren jiragen sama guda biyu kan wasu muhimman wurare a kudancin yankunan "Isra'ila" da ta mamaye.


Kungiyar Gwagwarmayar Musuluncin ta dauki alhakin harin da aka kai da sanyin safiyar Lahadi a tashar jiragen ruwa na "Eilat".


Kungiyar ta faɗa cewa za ta ci gaba da kai hari tare da lalata muhimman gine-gine a fadin kasashen da ta mamaye.

Post a Comment

Previous Post Next Post