Zamu Tsaya Tare Da Hezbullah Har Sai An Kwato Falasdinu, Al-quds: Kwamandan Quds IRGC

 


Kwamandan dakarun Quds na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya ce Iran za ta ci gaba da goyon bayan kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon har sai an sami 'yantar da Falasdinu da Kudus mai tsarki.


Birgediya Janar Esmail Qaani ya bayyana hakan ne a wani sakon ta'aziyya da ya aike a ranar Lahadi kan kisan da aka yi wa Sayyed Hassan Nasrallah, shugaban kungiyar Hizbullah mafi daɗewa, a wani hari da aka kai a kudancin Beirut a ranar Juma'a ta hanyar amfani da bama-bamai da Amurka ta kawo.


Ya ce shahadar ta Shugaban Hezbullah ta haifar da bakin ciki matuka a tsakanin dukkanin al'ummar Iran da kungiyoyin gwagwarmayar Musulunci da kuma 'yantattun al'ummar duniya.


Kwamandan na IRGC ya jaddada cewa Sayyid Nasrallah ya kwashe tsawon rayuwarsa yana yakar mafiya sharrin makiyan Musulunci da Alkur'ani mai girma, daga karshe kuma ya sadaukar da jininsa ga ma'abota kima na Musulunci da kuma tafarkin tallafawa al'ummar Palastinu da Lebanon da ake zalunta.


Ya kara da cewa, shugaban kungiyar Hizbullah mai hikima ya jagoranta sannan kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen yaki da 'yan ta'addar Daesh da Takfiriyya.


Bayan sanarwar da kungiyar Hizbullah ta yi na shahadar Sayyid Nasrallah, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce bangaren gwagwarmaya za su kara ƙaimi gurin murkushe gwamnatin sahyoniyawa.


Jagoran ya ce tushen da Nasrallah ya kafa a kasar Labanon tare da bayar da jagoranci ga sauran cibiyoyin iko ba zai gushe da rashin shiba, sai dai zaya karfafa da jininsa.


Allah madaukakin sarki ya karbi shahadar wannan babban Bawa Mujahidi da kuma sauran Shahidai ya kuma kawo karshen Isra'ila da masu goyon bayan ta a duk Inda Suke.

Post a Comment

Previous Post Next Post