Kungiyar gwagwarmayar Islama a Iraki ta ce ta kai sabbin hare-hare a yankunan Falasdinu da Isra'ila ta mamaye, inda suka kai hari da jirage marasa matuka "don goyon bayan Falasdinu da kuma Lebanon."
Kungiyar Gwagwarmayar Islama ta Iraki a cikin wata sanarwa da ta fitar a safiyar ranar Asabar ta ce a farmakin farko da ta kai ta kai hari a yankin arewacin Falasdinu da Isra'ila ta mamaye.
"A ci gaba da tafarkinmu na tinkarar mamaya, da goyon bayan al'ummarmu a Palastinu da Lebanon, da kuma mayar da martani ga kisan kiyashin da 'yan ta'addar suka aikata kan fararen hula da suka hada da yara, mata da tsofaffi, mayakan kungiyar Gwagwarmayar Islama a cikin kasar Iraki a ranar Asabar 28/09/2024, ta kai hari da jirage marasa matuka a wani wurin da sojoji suka mamaye a arewacin kasarmu,” in ji sanarwar.
A Hari na biyu kuma an kai shine kan wani muhimmin guri na Isra'ila a yankunan kudancin da ta mamaye da jirage marasa matuka.
Sanarwar ta ce, "Mayakan gwagwarmayar Musulunci a Iraki, a ranar Asabar 28/09/2024, sun kai hari a wani muhimmin wuri a kudancin yankunanmu da aka mamaye da jirage marasa matuka," in ji sanarwar.
Haka zalika Dakarun na Iraqi sun sha alwashin ci gaba da kai hare-hare kan guraren makiya.
A hari na uku, "mayakan Gwagwarmayar Islama a Iraki, da sanyin safiyar ranar Asabar 28/09/2024, a karo na uku, sun kai hari kan wata muhimmiyar manufa a arewacin yankunan da aka mamaye ta hanyar amfani da jirage marasa matuka."
Zamu cigaba da roqon Allah Ta'ala daya cigaba da baku Nasara da sauran 'Yan Gwagwarmayar Musulunci a duk Inda Suke.
