Hezbollah Tayi Watsi da Ikirarin da Isra'ila Keyi na Cewa ta Kaiwa Ma'ajiyar Makaman Hezbullah Hari A Gine-ginen Fararen Hula

 


Kungiyar Hizbullah ta yi kakkausar suka akan ikirarin da sojojin Isra'ila suka yi na cewa tana da makamai ko ma'ajiyar makamai a cikin gine-ginen Fararen hula a Beirut babban birnin kasar Labanon da ke fuskantar hare-haren wuce gona daga Isra'ilan.


Ofishin hulda da manema labarai na kungiyar gwagwarmayar Hezbullah dake ƙasar Lebanon ta fitar da wannan sanarwa a ranar Asabar bayan da sojojin Isra'ila suka yi ikirarin cewa suna kai hare-hare kan "makaman kungiyar Hizbullah… da ke karkashin gine-ginen Fararen hula" a kudancin Beirut.


"Ikirarin makiya game da kasancewar makamai ko ma'ajiyar makamai a cikin gine-ginen farar hula da harin bam da aka kai a yankin kudancin kasar karya ne," in ji ofishin.


Hare-haren sun auna gine-gine da dama a unguwannin al-Hadath da Laylaki a yankin Dahiyeh na Beirut.


Kungiyar Hizbullah dai tana mayar da martani ga wannan ta'addancin tare da daukar matakan ramuwar gayya yadda ya kamata.


Muna roqon Allah daya taimaki Mujahidun ya basu Nasara, ya kuma karbi shahadar wadanda suka rasa rayukansu.

Post a Comment

Previous Post Next Post