Jakadan kasar Sin na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan fashewar na'urorin sadarwa na baya-bayan nan a kasar Lebanon, yana mai bayyana kaduwa da tsananin damuwarsa kan hare-haren, wanda Ƙasar Lebanon da kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah suka dora alhakinsa kan Isra'ila.
Akalla mutane 37 da suka hada da fararen hula ne aka kashe tare da jikkata wasu dubbai a ranakun Talata da Laraba a lokacin da Na'urorin Pagers da Walkie walkie suka fashe a wurare da dama a fadin kasar Lebanon.
Wakilin kasar Sin Fu Cong, wanda yake magana a taron kwamitin sulhu na MDD da aka gudanar a ranar Juma'a, ya ce "Wannan Hare-haren wuce gona da iri ne da cin zarafi ga 'yancin kasar Lebanon.
Jami'in diflomasiyyar ya soki hare-haren soji da Isra'ila ke yi a Gaza da kuma take hakkin kasar Lebanon, yana mai kira ga Isra'ila da ta dakatar da abinda take yi, sannan yayi kira ga dukkan bangarorin da su yi taka-tsan-tsan don hana ci gaba da barkewar rikici.
