Akalla Mutane 51 Ne Suka Mutu Sakamakon Fashewar Gurin Haƙar Ma'adinan Kwal a Iran

 


Fashewar wata mahakar kwal ta yi sanadin mutuwar mutane akalla 51 tare da jikkata wasu 20 a birnin Tabas na kasar Iran a lardin Khorasan ta Kudu.


 Mohammad-Ali Akhondi, babban darakta na sashen kula da rikice-rikice na lardin, ya bayyana ayau Lahadi cewa hatsarin ya faru ne sakamakon fashewar iskar gas na methane a wasu sassa biyu na mahakar ma'adinan a daren Asabar.


Akalla ma’aikata 51 ne suka mutu sakamakon saurin fitowar methane da carbon monoxide, ya ce ana sa ran adadin wadanda suka mutu zai karu yayin da ayyukan ceto ke da wuyar gudanar da aikin saboda yanayin da ke karkashin kasa.


 Jami'in ya kara da cewa, an karfafa aikin ceto cikin gaggawa, yana mai karawa da cewa "amma gaskiyar magana ita ce aiki ne mai wahala a ceto wadanda suka jikkata daga zurfin mita 700 a diagonal da kuma mita 250 a tsaye a karkashin kasa."


Akwai ma'aikata 69 a cikin shingen a lokacin fashewar mahakar ma'adinan da ke garin Tabas, wani birni a tsakiyar gabashin Iran.


Shugaba Pezeshkian ya ba da umarnin gudanar da bincike


 Shugaba Masoud Pezeshkian ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin, a cewar shugaban kwamitin yada labarai na gwamnatinsa.


Elyas Hazrati ya fada a yau Lahadi cewa ministocin masana'antu da na kwadago sun nufi Tabas don gudanar da tarurrukan da suka dace da kuma ba da umarnin daukar matakan da ake bukata bayan afkuwar lamarin.


Ministan cikin gida Eskandar Mo’meni shi ma yana bin wannan batu, in ji Hazrati, ya kuma kara da cewa shi da kansa ya kuma tattauna ta wayar tarho da gwamnan lardin domin samun sabbin bayanai game da halin da ake ciki a wurin da fashewar ta auku.

Post a Comment

Previous Post Next Post