Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta lashi takobin tsayawa tsayin daka a kokarin da take yi na kare kasar a tunkarar hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi, tare da yin alkawarin daukar fansa kan gwamnatin kasar.
Shugaban Majalisar Zartarwar Hizbullah Sayyed Hashem Safieddine ya ce "Za mu fada wa makiya yahudawan sahyoniya cewa ba za mu ji tsoro ko ja da baya ba."
Ya kara da cewa, "Muna gargadin dukkanin kwamandojin sojojin makiya cewa a shirye muke," in ji shi, yayin wani bikin jana'izar da aka yi wa 'ya'yan kungiyar, wadanda suka yi shahada a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.
"Kowa ya tabbatar da cewa Gwagwarmaya ce ke da rinjaye, kuma za ta iya kai wa abokan gaba hari," in ji jami'in.
Kalaman nasa sun zo ne kwana guda bayan wasu fashe-fashe da aka kai a fadin kasar, lamarin da ya yi sanadin shahadar mutane akalla 12, ciki har da yara biyu, tare da jikkata wasu kusan 3,000.
