Sojojin Isra'ila 15 ne Suka Mutu, Jikkata Yayin da Hezbollah ta Kai Hari a Wani Sansanin Soji

 


Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ta kai hari kan wani sansanin sojin Isra'ila da ke arewa maso gabashin yankunan Falasdinawa da ta mamaye, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar sojojin mamaya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Alhamis, Hezbollah ta ce ta kai hari kan sansanin soja na Al-Marj da ke kusa da kan iyakar Lebanon da yankunan da aka mamaye da "makamai da suka dace" wanda ya haddasa "mutuwa tare da jikkata da dama" a tsakanin sojojin Isra'ila.  

Kungiyar Hizbullah ta kuma jaddada cewa harin ya zo ne domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu a zirin Gaza da kuma tsayin daka.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun bayar da rahoton cewa sojoji biyu ne suka mutu sannan wasu akalla 13 suka jikkata bayan da wasu makamai masu linzami guda biyu da aka harbo daga kudancin kasar Lebanon suka afkawa yankunan da aka mamaye.

Harin ya zo ne bayan wani harin ta'addanci da Isra'ila ta kai kan mutanen Lebanon wanda yayi sanadin shahadar mutane fiye da fiye da 30 tare da jikkata wasu 3,250.

Post a Comment

Previous Post Next Post