'Yan Muqawama na Iraqi Sun Ce Ƙidayar Kai Hare Hare ga Matsugunnan Isra'ila ta Soma

 


Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah al-Nujaba Akram al-Kaabi ya sha alwashin kai hari kan dukkanin matsugunan yahudawan sahyoniya.


 Dangane da harin yanar gizo da yahudawan sahyuniya suka kai wa kasar Labanon, Akram al-Kaabi ya fada a yammacin jiya Talata cewa kungiyar za ta bude wuta kan dukkanin matsugunan yahudawan sahyoniya a daukacin kasar Falasdinu da ta mamaye.


Ya kara da cewa dakarun Iraqi sun shirya tsaf domin yin amfani da sabbin makamai, makamai masu linzami, da jirage marasa matuka.


A halin da ake ciki kuma, ofishin kungiyar Hizbullah al-Nujaba da ke birnin Tehran a cikin wata sanarwa da ta fitar ta sanar da cewa, hare-haren ta'addanci ba su da wani tasiri face karfafawa tare da martaba mayakan gwagwarmaya.


Yayin da suke bayyana cikakken goyon bayansu ga 'yancin al'ummar Larabawa, al-Nujaba ta jaddada goyon bayan Hezbullah a kan yahudawan sahyoniya, Amurka da kawayenta.


Kafofin yada labaran kasashen Yamma sun kammala da cewa hukumar leken asiri ta Isra'ila Mossad ta dasa bama-bamai a cikin batura na pagers da suka fashe a kasar Labanon, lamarin da ya yi sanadin mutuwa da jikkata a yammacin ƙasar Lebanon a ranar Talata.


 Majiyar ta ce Mossad ta samu nasarar gyara na'urorin sadarwar na kungiyar Hizbullah kafin mika su ga wannan kungiyar, inda ta kara da cewa Mossad ta sanya wasu abubuwa masu fashewa da ake kira pentaerythritol tetranitrate (PETN) a cikin batura na na'urorin, wadanda suka fashe a lokacin da Temperature ta karu.


 Wannan ta'addancin da gwamnatin sahyoniya ta yi ya yi sanadiyyar shahidai 11 tare da jikkata wasu sama da 2,000.

Post a Comment

Previous Post Next Post