Dubban 'yan kungiyar gwagwarmayar Hezbullah ta kasar Lebanon da kuma fararen hula ne suka mutu ko kuma suka jikkata bayan da na'urorin sadarwa wanda aka fi sani da "Pager", suka dinga fashewa a wurare daban-daban a fadin kasar a ranar Talata.
A cikin sabon rahotonta, ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta ce akalla mutane tara ne suka mutu, yayin da wasu 2,800 suka samu raunuka, sakamakon fashewar wasu abubuwa da aka fara samun rahoton su a yankunan kudancin birnin Beirut.
Ma'aikatar ta ce "an tura majinyata zuwa yankuna daban-daban na Lebanon saboda asibitocin kudancin Lebanon sun cika."
Daga cikin wadanda aka kashe har da wata yarinya ‘yar shekara 9 da kuma dan wani dan majalisa mai alaka da kungiyar Hizbullah, kamar yadda wakiliyar tashar talbijin ta Press TV a Beirut Mariam Saleh ta bayyana a wani rahoto daga babban birnin kasar Labanon.
An bayyana cewa yarinyar data Rasun sunanta Fatima Jafar Abdullah yayin da saurayin kuma aka bayyana shi a matsayin Mahdi Ammar.
Jakadan Iran a Lebanon, Mojtaba Amani, shi ma yana cikin wadanda suka jikkata. Matarsa ta yi amfani da shafin X, wadda akafi sani a baya da Twitter, don tabbatar da rauninsa a fashewar Na'urar mai suna "pager" amma ta ce yanayinsa da sauqi.
Saleh ta ce wasu daga cikin mutanen da ke dauke da na'urar "Pager" sun lura da cewa tana yin zafi kafin ta fashe, ta kara da cewa Isra'ilawa na cikin shirin ko-ta-kwana, suna sa ran mayar da martani daga kungiyar Hizbullah.
Muna roqon Allah daya ba wadanda suka samu Raunuka lafiya, ya kuma karbi shahadar wadanda suka rasa rayukansu.
