Dakarun Yemen sun ce sun harba wani sabon makami mai linzami na Ballistic a kudancin Tel Aviv

 


Dakarun Yaman sun kai hari kan wani guri na Haramtacciyar Kasar Isra'ila a kusa da birnin Tel Aviv da wani sabon makami mai linzami bayan da gwamnatin ta 'yan mamaya ta kasa daƙile harin na wani makami mai linzami mai cin dogon zango.

Kakakin rundunar sojan kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Saree ya sanar a cikin wani takaitaccen bayani da aka watsa ta gidan talabijin a yau Lahadi cewa, dakarun makami mai linzami sun kai wani hari mai inganci kan wani wuri na Isra'ila dake a yankin Jaffa da ke kudancin birnin Tel Aviv a yankin Falasɗinawa da suka mamaye.


“The operation was carried out with a new hypersonic ballistic missile that managed to reach its target, and the enemy’s defense systems failed to intercept and confront it,” Saree said.


Saree ya ce "An kai harin ne da wani sabon makami mai linzami na Ballistic wanda ya yi nasarar kaiwa ga inda aka aika shi, yayinda tsarin tsaron abokan gaba ya kasa tare shi da kuma tunkararshi" in ji Saree.


“It crossed a distance of 2040 km in 11 and a half minutes, and caused a state of fear and panic among the Zionists, as more than two million Zionists headed to shelters for the first time in the history of the Israeli enemy.”


"Makamin yaci tazarar kilomita 2040 a cikin mintuna 11 da rabi, wanda ya haifar da yanayi na tsoro da firgici a tsakanin yahudawan sahyoniyan, yayin da sama da 'yan sahayoniya miliyan biyu suka nufi mafaka a karon farko a tarihin makiya."

Kakakin ya ce, wannan farmakin wani bangare ne kashi na biyar na yaƙin da ake yi da makiya Isra'ila, kuma ya yi nasarar kaiwa inda aka aika shi ta hanyar shawo kan duk wani cikas, ciki har da tsarin tsaron Amurka da Isra'ila na kan kasa da teku.

Post a Comment

Previous Post Next Post