Jirgin ruwan Amurka USS Theodore Roosevelt ya janye daga yankin gabas ta tsakiya bayan ya kwashe watanni biyu yana aiki ba tare da cimma manufarsa ba. Jirgin dai ya kaucewa yankin da Dakarun Yemen ke gudanar da Ayyukan su, saboda fargabar hare-haren da sojojin Yaman ke kaiwa domin goyon bayan Al'ummar Gaza.
Hakan dai ya nuna gagarumar gazawar sojojin ruwan Amurka, wadanda ke fafutukar tunkarar karfin soji na kasar Yemen. Sakataren harkokin wajen Amurka ya amince cewa tsagaita wuta a Gaza ita kadai ce hanya daya tilo da za ta kwantar da hankulan al'amura a tekun Bahar Maliya.
Ayyukan na Dakarun Yemen sun haifar da tarnaki a fannin tattalin arziki, inda masu sayar da kayayyaki na Biritaniya ke fuskantar tsadar kayayyaki da kuma tsaiko sakamakon sake safarar jiragen ruwa. Kamfanonin inshora kuma sun ƙi rufe jiragen ruwa da ke da alaƙa da Isra'ila, Amurka, da Biritaniya.
Dakarun kasar Yemen sun harbo jiragen yakin Amurka guda 9 na zamani tare da ci gaba da aiwatar da dokar hana zirga-zirgar jiragen ruwa ga isa tashar jiragen ruwa na Isra'ila. Rundunar sojin ruwan Amurka ta kashe biliyoyin kudade wajen sayan makamai ba tare da samun gagarumar nasara ba.
