Kasashen Yamma sun amince da gagarumar gazawar su a tekun Bahar Maliya, inda suka bayyana gazawarsu wajen tabbatar da cigaban zirga-zirgar jiragen ruwa zuwa Isra'ila cikin aminci, biyo bayan killacen da kasar Yemen ta yi kan jiragen ruwan da ke kan hanyar zuwa tashar jiragen ruwa na yankunan Falasɗinawa da aka mamaye.
Jaridar The Telegraph ta kasar Burtaniya ta tabbatar da cewa gazawar kasashen yammacin Turai a tekun Bahar Maliya ya shafi kayayyakin da Birtaniyya ke shigowa da su kasar, wanda hakan ya jawo babbar matsala ga ƙasar.
Ta yi bayanin cewa gazawar yammacin Turai ya tilastawa masu Jigilar kaya zuwa Birtaniya dasu sake hanya domin zuwa Biritaniya, inda suke kewayawa ta Cape of Good Hope, wanda hanya ce mai tsayi, mai tsada, kuma mafi hatsari.
Jaridar ta kuma ce Biritaniya na shigo da kaso 90 cikin 100 na kayayyakinta ta teku, hakan yasa dukkan wani cikas gurin jigilar kayayyakin zai haifar da hauhawar farashin kayayyaki.
Jaridar ta ce kamfanonin sufurin jiragen ruwa suna ba da ƙarin kuɗi ga masu amfani da su saboda ƙarin inshora da farashin mai.
Jaridar ta kuma ce kokarin da kasashen Amurka, Birtaniya da Turai suka yi na tabbatar da hanyoyin jigilar kayayyaki ya ci tura, kuma ba za su iya dakatar da ayyukan Yemen ba.
Bugu da kari, sojojin ruwan Burtaniya ba za su iya kare jiragen da ke zuwa Isra'ila ba saboda ba su da isassun jiragen yaki.
Jaridar Telegraph ta bayyana cewa watsin da sojojin ruwan Amurka suka yi ga jirgin ruwan dakon mai mai suna MV Sounion da ya shafe makwanni biyu yana cin wuta, na nuni da ja da baya da Amurka ta yi daga kare zirga-zirgar jiragen ruwa.
Rahoton na Telegraph ya zo ne kwanaki bayan da jirgin yakin Amurka Roosevelt ya janye daga Gabas ta Tsakiya, bayan da ya shafe watanni bai samu shiga yankin da Dakarun Yemen ke gudanar da ayyukan su ba a cikin tekun Bahar Maliya.
A ranar Juma'ar da ta gabata, tawagar kawancen kasashen yammacin Turai, mai suna Aspides, ta tabbatar da cewa an kaiwa jirgin ruwan Sounion hari a cikin tekun Bahar Maliya, saidai rahotanni sun nuna cewa jirgin yana lafiya.
A cikin 'yan watannin da suka gabata, Dakarun Yaman sun samu gagarumar nasara a kan jiragen ruwa na Amurka da Birtaniya da kuma Isra'ila.
Wanda waɗannan hare haren suka haddasa fatarar tashar jiragen ruwa ta Um Rashrash, wacce aka fi sani da Eilat, bayan da jiragen ruwa suka gaza isa gare ta.
Bugu da ƙari, waɗannan ayyukan sun tilasta wa jirgin ruwan Amurka Eisenhower guduwa daga Tekun Bahar Maliya, inda Jirgin ruwan Roosevelt ya biyo baya, kuma ya yi sanadin nutsewa da lalata da yawa daga cikin jiragen ruwa.
Wadannan Nasarori na sojojin ruwan Yaman sunba manazarta mamaki, kasancewar a da ba a dauki Yemen a matsayin mai karfin sojin ruwa ba.
Dakarun Yaman sun sha alwashin ci gaba da gudanar da ayyukansu muddin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta ci gaba da yaki da kuma kawanya a kan yankin Falasdinu.
