Kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labanon ta harba makamai masu linzami a wani sansanin sojin Isra'ila a matsayin ramuwar gayya kan wani mummunan harin da aka kai kan yankunan kasar Lebanon.
Hezbollah ta ce ta harba makaman roka na Katyusha a “babban sansanin tsaron sama na makamai masu linzami” na rundunar sojojin Arewa a barikin Berea kusa da birnin Safed da ke arewacin yankunan da aka mamaye da sanyin safiyar Juma’a.
Rahotanni sun ce harin ya haddasa tashin gobara tare da janyo katsewar wutar lantarki.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce an harba wasu rokoki guda 20 daga kasar Lebanon, inda suka ce an tarbe yawancinsu.
Wannan dai shi ne hari na biyu da aka kai wa barikin na Berea, wanda ke da tazarar kilomita 12 daga kan iyakar kasar Lebanon, tun bayan da aka tsananta musayar wuta tsakanin ‘yan gwagwarmaya da gwamnatin mamaya a watan Oktoban da ya gabata.
Isra'ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba bayan da kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta Falasdinu ta kaddamar da Harin Guguwar Al-Aqsa a kan 'yan mamaya a matsayin ramuwar gayya kan irin ta'asar da suke ci gaba da yi kan al'ummar Falasɗinu.
Yayin da Gwamnatin ta mamayar ta yiwa yankin ƙawanya, inda ta katse mai, wutar lantarki, abinci da ruwa ga Falasdinawa sama da miliyan biyu da ke zaune a Gaza.
Tun bayan fara kai farmakin, gwamnatin Tel Aviv ta kashe Falasdinawa 41,118 tare da jikkata wasu kusan 95,125.
