Beijing ta lashi takobin "murkushe" duk wani kutse da kasashen waje ke yi a cikin ikonta, ciki har da tekun kudancin China, a cewar wani babban jami'in sojan kasar Sin.
Kasar Sin tana da'awar Mallakar kusan dukkanin tekun Kudancin China, yankin da ya mamaye yankunan Philippines, Malaysia, Vietnam da Brunei.
Laftanar Janar He Lei na rundunar sojojin kasar Sin ya jaddada matsayin kasar Sin, yana mai cewa, "Muna fatan tekun kudancin kasar Sin ya kasance tekun zaman lafiya," a yayin ganawa da manema labarai a gefen dandalin Xiangshan na Beijing karo na 11, wani babban taro da ya mayar da hankali kan tsaro.
Amurka bata amince da matakin da China ta dauka a cikin ruwan da ake takaddama a kai ba. Amurka na kallon China a matsayin mai tada hankali, yayin da China ke kallon kanta a matsayin mai kare hakkinta.
Ko da yake Amurka batayi da'awar yankin na kan ruwa ba, amma tana gudanar da sintiri akai-akai a can, ita kadai ko tare da kawayenta, ciki har da Philippines, domin fusatar da kasar Sin.
"Idan Amurka ta motsa 'yan barandanta a bayan fage, ko ta tura kasashe zuwa gaba, ko kuma ita Amurkar da kanta ta fito a gaba, to mu a cikin rundunar 'yantar da jama'ar Sin ... ba za mu taba yin hakuri ba. ” Laftanar Janar ya yi gargadin.
"Mu a cikin rundunar 'yantar da jama'ar kasar Sin, za mu yanke shawarar murkushe duk wani katsalandan na kasashen ketare kan yankin mu.
