Shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, Yahya Sinwar ya ce shahadar magabacinsa Ismail Haniyeh da sauran mayakan Falasdinawa zata kara karfafa gwagwarmayar da suke yi na kawar da gwamnatin Isra'ila.
Sinwar ya bayyana hakan ne a cikin wasu sakonnin da ya aike wa jami'an musulmi daban-daban, wadanda suka jajantawa kungiyar dangane da shahadar Haniyyah.
An kashe tsohon shugaban na Falasdinawa ne a karshen watan Yuli a wani hari da aka kai masa a Tehran babban birnin kasar Iran, inda ya je domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Masoud Pezeshkian.
"Wannan tsarkakakken jini da ayarin shahidai masu albarka za su kara mana dagewa ne kawai wajen tunkarar mamayar yahudawan sahyoniya har sai an kore ta da kuma shafe ta daga doron kasa," in ji Sinwar a cikin sakonnin.
Ya kara da cewa, irin wannan nasara ta karshe, za ta biyo bayan Palasdinawa ne su kafa kasarsu mai cin gashin kanta tare da (birni mai tsarki) al-Quds a matsayin babban birninsa.
Shahadar Haniyeh ta tabbatar da cewa "jinin shugabanninmu da mayakanmu bai fi jinin al'ummar Falasdinu daraja ba," in ji shugaban Hamas.
