Dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun bude wani sabon sansanin sojin sama a arewa maso yammacin kasar Iran kusa da kan iyaka da Turkiyya.
Kwamandan IRGC Manjo Janar Hossein Salami ya bude sabon sansani mai suna Shahid Manjo Janar Mahmoudabadi a birnin Urmia, babban birnin lardin yammacin Azabaijan na Iran a ranar Laraba.
Babban kwamandan IRGC ya bayyana a wurin bude taron cewa Iran na fuskantar barazana a yankin arewa maso yammacinta daga makiya da kuma masu adawa da juyin juya halin Musulunci.
Birgediya Janar Ali Akbar PourJamshidian ya ce kaddamar da sabon sansanin sojin sama na da nufin bunkasa karfin tsaron kasar Iran, yana mai cewa matakin zai yi matukar amfani ga kasar da sojojinta.
Tags
Iran
