'Yar takarar jam'iyyar Democrat Kamala Harris da dan takarar jam'iyyar Republican Donald Trump sun fafata a muhawararsu ta farko ta shugaban kasa da kafar yada labarai ta ABC ta shirya a zaben watan Nuwamba.
A cewar wakilin IRNA, Harris da Trump sun yi musafaha a farkon muhawarar wacce takai tsawon mintuna 90 da aka watsa a gidan talabijin a cibiyar kundin tsarin mulkin kasar da ke birnin Philadelphia na jihar Pennsylvania a daren ranar Talata da ta gabata.
Yayin da suke amsa tambayar da aka yi kan tattalin arziki, Harris da Trump sun zargi juna da cewa ba su da wani shiri na bunkasar tattalin arziki.
Na gina mafi karfin tattalin arziki a Amurka sau daya a ofis kuma zan sake maimaita wannan nasarar, in ji Trump, yana mai kara da cewa "muna da mummunan tattalin arziki saboda hauhawar farashin kayayyaki; miliyoyin mutane suna zuwa Amurka suna sace mana ayyukanmu. Biden ya bar su."
Ya kara da'awar cewa yawancin masana tattalin arziki suna ɗaukar shirye-shiryensa a matsayin mafi kyawu, yayin da ita kuma Harris ba tada wani shiri kuma tana son ci gaba akan hanyar da Biden yake.
Harris ta mayar da martani da cewa Trump ba shi da tsare-tsare kuma yana son rage haraji ga masu hannu da shuni kadai.
Ina so in rage haraji da tallafawa tattalin arzikin Amurka. Ni yarinya ce dake cikin matsakaitan mutane. Zan yi wani shiri na daga darajar rayuwar wannan kungiya. Na yi imani da mafarkai da burin jama'ar Amurka kuma ina da niyyar gina tattalin arziki bisa dama.
Mataimakiyar shugaban ƙasan ta kara da cewa: Ina son kananan sana'o'i. Ina so in ba da dala 50,000 a matsayin hutun haraji ga masu farawa, amma abokin hamayya na yana son ba da hutun haraji ga masu biliyoyi.
A karkashin Trump, Amurka ta sami mafi munin rashin aikin yi. Gwamnatin Trump ta haifar da gibin kasuwanci mafi girma a tarihin Amurka, ta kara yin tir da batun tattalin arziki.
Trump ya sake yin alkawarin sanya wa wasu kasashe haraji, yana mai cewa "wannan harajin haraji ne na biyan kudaden da Amurka ta yi wa duniya."
Tsohon shugaban na Amurka ya yi nuni da kasar Sin inda ya ce manufofin gwamnatinsa na iya kawo biliyoyin daloli zuwa asusun Amurka daga kasar Sin ta hanyar sanya haraji.
