Guy Hazoot, Janar na Isra’ila mai ritaya, ya bayyana cewa Isra’ila ta rasa yadda za ta iya hana akai mata hare-hare, kuma a yanzu ana kallonta a matsayin "yaron da aka yi wa dukan tsiya da wulakanci a cikin yara" a Gabas ta Tsakiya, kamar yadda Yedioth Ahronoth ya ruwaito.
A wani taro na jami'an soji, Hazoot ya yi nuni da cewa 'a kalla rabin 'yan kungiyar Hamas har yanzu suna raye, yayin da ake ci gaba da tsare da dama daga cikin 'yan Isra'ila, a lokacin da yake magana dangane da halin da ake ciki a Gaza.
Mafi girman gazawa tun daga ranar 7 ga Oktoba ya ta'allaka ne kan gudanar da yakin Gaza," in ji Hazoot.
Ya kara da cewa "Isra'ila" tana barci a lokacin da 'yan gwagwarmayar Falasdinu suka kai farmaki kan matsugunansu a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda hakan ya matukar kunyatasu a lokacin.
Ya yi nuni da cewa "duk wanda ke son wulakanta 'Isra'ila' sai kawai ya kaddamar da Hari," yayin da yake nuni da hare haren makamai masu linzami da Jirage marasa matuka da aka harba zuwa "Isra'ila" daga Iran, Lebanon, Yemen da Iraki.
Muna roqon Allah daya cigaba da wulakanta su, ya kuma kawo karshen su baki daya da gaggawa.
