Falasdinawa 19 Sun yi Shahada Sakamakon Harin Da Isra'ila Ta Kai A Zirin Gaza


 Falasdinawa 19 ne suka yi shahada sakamakon wani hari da jirgin yakin Isra'ila ya kai a wani gida da ke arewacin Gaza, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito.


Jiragen yakin gwamnatin sahyoniyawan sun kai hari a wani gida da ke Beit Lahia da ke arewacin Zirin Gaza inda suka yi sanadin shahadar Falasdinawa 11 kamar yadda kafar yada labarai ta Shahab ta Falasdinu ta rawaito a yau Alhamis.


Bugu da kari, jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kuma yi ruwan bama-bamai a wani gida da ke unguwar Tal Al-Zaatar da ke gabashin Jabalia a arewacin zirin Gaza, inda suka kashe Falasdinawa biyu tare da jikkata wasu adadi.


Hakazalika jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra'ila sun kai hari kan wani gida a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Maghazi da ke tsakiyar Gaza, inda suka kashe Falasdinawa shida.


Tun da farko a ranar Laraba, ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar da cewa Falasdinawa 40,223 ne suka yi shahada a hare-haren da Isra'ila ke kai wa zirin Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Post a Comment

Previous Post Next Post