Kungiyar gwagwarmayar Islama a Iraki ta kai sabbin hare-hare a kan guraren sojojin Isra'ila dake tuddan Golan na Siriya da suka mamaye.
Wata kungiyar gwagwarmaya ta Iraqi, a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin Lahadi, ta ce hare-haren na goyon bayan Falasdinawa ne da kuma mayar da martani ga kisan gillar da "Isra'ila" ta yi wa fararen hula a Gaza.
Kungiyar ta Gwagwarmayar Islama ta sha yin gargadin cewa idan aka ci gaba da yin kisan kare dangi a Gaza, mayakanta za su kara kaimi wajen yaki da "Isra'ila".
Kungiyoyin gwagwarmaya na yanki sun sha kai hare-hare a gurare masu matukar mahimmanci na "Isra'ila" a cikin Falasdinu da ta mamaye.
Dakarun na Iraki sun kai hare-hare da dama kan cibiyoyin soji da Amurka ke gudanarwa a kasashen Iraki da Siriya a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna kyama ga Amurka a yankin, dangane da goyon bayan da Washington ke ba wa yakin kisan kare dangin da "Isra'ila" keyi a Gaza, wanda ya zuwa yanzu ya yi sanadin shahadar fiye da Falasdinawa 40000, galibi mata da yara.
Dakarun na Islama sun harba makamai masu linzami guda hudu daga kasar Iraki inda suka hari sansanin sojin Amurka da ke yankin Conoco da ke karkashin ikon Washington a gabashin Syria."
.jpg)