Dakarun kasar Yemen sun ce sun kai sabbin hare-hare kan wasu jiragen ruwa guda hudu da ke da alaka da Amurka, Birtaniya da kuma Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila da makamai masu linzami.
Kamfanin dillancin labaran Tasa na kasar Rasha a jiya Litinin ya nakalto Yahya Saree kakakin rundunar sojin kasar Yemen yana cewa, an kai wadannan hare-haren ne kan jirgin ruwan kwantena mai suna MSC Unific VI, da wasu tankokin mai guda biyu Delonix da Lucky Silver da kuma jirgin ruwa mai ɗaukar kaya Anvil Point.
Saree ya kara da cewa dakarun kasar Yemen sun yi amfani da makami mai linzami wajen kai farmaki kan wadannan jiragen ruwa.
A lokacin da aka kai harin, MSC Unified yana cikin Tekun Arabiya, jirgin ruwan dakon mai na Delonix yana cikin tekun Bahar Maliya, jirgin mai Lucky Silver yana cikin Tekun Mediterrenean, sannan kuma jirgin Anvil Point yana cikin Tekun Indiya, in ji kakakin Yemen inda yake bayar da cikakken bayani.
Kakakin ya kuma ce wannan shi ne karo na biyu da aka kai hari akan Jirgin Delonix a cikin makon da ya gabata.
A 'yan kwanakin da suka gabata ne dakarun kasar Yemen suka sanar da cewa, a wani samame na hadin gwiwa da kungiyar gwagwarmayar Islama a Iraki sun kai hari kan jirgin ruwan Waler mai dakon mai, Johannes Maersk mai ɗaukar kaya, da kuma Jirgin Ruwan Delonix na dakon sinadarai da kuma Jirgin Ruwan Ioannis.
Sojojin Yamen ɗin sun dinga kai hare hare kan jiragen ruwan HKI ko kuma Jiragen Ruwan da ke kan hanyar zuwa tashar jiragen ruwa a yankunan da aka mamaye a cikin tekun Bahar Maliya da mashigin Bab al-Mandab a cikin watannin da suka gabata domin nuna goyon bayansu ga gwagwarmayar Palasdinawa a zirin Gaza.
Rundunar sojin Yaman tace zata ci gaba da kai hare hare har sai gwamnatin Isra'ila ta daina kai hare-hare a Gaza. Haka kuma ta zafafa kai hare-hare kan jiragen ruwa na Amurka da na Birtaniya a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren sama da kasashen biyu ke kaiwa kasar Yemen domin kare muradun Isra'ila a yankin.
