Dakarun muslunci na kasar Labanon sun sake kai hari a cibiyar tarukan sojojin yahudawan sahyuniya a arewacin kasar Palastinu da ta mamaye.2024
Sanarwar da kafar yada labaran Hezbollah ta fitar ta ce "Mun kai hari kan tarurrukan sojojin mamaya dake a Granot da makamin da ya dace, wanda ya afkawa wurin kai tsaye."
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Labanon ta kara da cewa an kai wannan harin ne domin tallafa wa al'ummar Palastinu masu tsayin daka a yankin Zirin Gaza da kuma goyon bayan gwagwarmayar Palastinawa masu jaruntaka da mutunci.
