Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta kai wani mummunan hari da makami mai linzami kan matsugunan yahudawan sahyoniya da ke Ashkelon kusa da zirin Gaza.
A cewar gidan talabijin na Aljazeera, amsa kuwwa dake alamta zuwan Rokoki tayi ƙara a Kissufim da ke kusa da Gaza.
Gidan rediyon HKI ya sanar da cewa an ji karar amsa kuwwa har sau bakwai cikin mintuna 15 a matsugunan yahudawan sahyoniya da ke kewayen zirin Gaza.
Kafofin yada labaran Isra'ila sun kuma bayar da rahoton cewa an kai hare-haren rokoki kan Ein HaShlosha kibbutz da ke kusa da zirin Gaza.
A cewar gidan rediyon sojojin Isra'ila, an harba rokoki 20 daga zirin Gaza zuwa matsugunan Ashkelon.
Tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata, akalla Falasdinawa 37,765 galibi mata da kananan yara ne aka kashe a yankin Zirin Gaza a yakin kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi kan yankin Falasdinu da aka yi wa kawanya.
