Bayan Shekaru Hudu Ƙasar Turkiyya ta Dawo da Shigo da Mai Daga Iran

 


Wani rahoto da ofishin kididdigar kungiyar Tarayyar Turai (Eurostat) ta fitar ya nuna cewa, Turkiyya sake shigo da mai daga kasar Iran a karon farko bayan shekaru hudu.


 Rahoton ya kuma nuna cewa wasu jami'ai biyu na kungiyar Tarayyar Turai suma sun shigo da man kasar Iran a shekarar 2024 duk da takunkumin da Amurka ta kakabawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.


Duk da Bulgaria memba ce ta Tarayyar Turai (EU), ta shigo da ton 314 na mai daga Iran daga watan Janairu zuwa Maris a shekarar 2024, wanda ya nuna karuwar kashi 113% idan aka kwatanta da ton 147 da aka shigo dashi a bara, a cewar rahoton.


 Poland ma wadda itama memba ce ta EU, ta karbi ton 19 na mai na Iran a cikin Watan Maris 2024.


Duk da cewa dan kadan ne, man da mambobin kungiyar EU ke shigowa da shi na nuni da cewa takunkumin da aka kakabawa Iran ya yi matukar matsin lamba ga bangaren makamashi na kungiyar ta EU, lamarin da ya sa wasu mambobin kungiyar suka bijirewa ko watsi da takunkumin.

Post a Comment

Previous Post Next Post