Ƙasar Turkiyya Ta ki Barin Jirgin Isra'ila ya Ƙara Mai: Rahoto

 


Kafafen yada labarai sun ruwaito cewa, Ƙasar Turkiyya ta ki sawa Jirgin saman Isra'ila El Al wanda ya taso daga Warsaw zuwa Tel aviv mai.


 Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin HKI ta ce ba a ba wa jirgin Warsaw zuwa Tel Aviv damar shan mai ba a filin jirgin saman Antalya, bayan da ya yi saukar gaggawa don sauke wani fasinja saboda dalilai na lafiya.


Sanarwar da El Al ta fitar ta ce, ma'aikatan Turkiyya dake filin jirgin saman Antalya sun ki amincewa da sama jirgin nasu mai, jirgin mai lamba LY5102 kafin ya tashi zuwa Isra'ila.


 "Ma'aikatan sun ki sawa jirgin mai duk da cewa lamarin lafiya ne," in ji su.


Adadin mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa a zirin Gaza ya karu zuwa 37,877 a cewar hukumomin lafiya na Gaza a wata sanarwa a ranar Lahadi.

Post a Comment

Previous Post Next Post