Masu zanga-zanga a Isra'ila sun rufe wata babbar hanya a birnin Tel Aviv domin nuna adawa da manufofin firaministan gwamnatin Sahayoniya Benjamin Netanyahu.
Tashar yada labarai ta Al Mayadeen ta bayar da rahoton cewa, masu zanga-zangar sun nuna adawa da manufofin Netanyahu ta hanyar toshe babbar hanya mai lamba 40, wadda ita ce hanya mafi tsawo a yankunan da aka mamaye bayan babbar hanya ta mai lamba 90.
Babbar hanya mai lamba 40 wadda keda tsawon kilomita 302 ta hade arewacin Tel Aviv zuwa kudancinta, kuma masu zanga-zangar sun tare ta a kusa da mahadar Magshimim da ke gabashin birnin Tel Aviv.
Masu zanga-zangar na HKI sun hada da iyalan ‘yan HKI wadanda akai garkuwa da su a Gaza, wanda dama kuma a ranar Laraba sun toshe babbar hanyar Tel Aviv, inda suka bukaci da a yi musanyar fursunoni da kungiyar gwagwarmayar Hamas ta Falasdinu.
A cewar kafar yada labarai ta Isra'ila KAN, Iyalan wadanda aka kaman sun tare babbar hanyar Ayalon da ta hada Tel Aviv da sauran birane da kuma garuruwan da ke kewaye."
