Wata Jaridar Isra'ila ta yi gargadi game da fadada yakin da ake yi da kasar Labanon, tana mai cewa sakamakon Babban yaƙi da kungiyar Hizbullah babu makawa zai haifar da rashin Nasara ga Isra'ila.
Muddin Isra'ila ta fadada yakin zuwa Lebanon tare da kai hare-hare ta kasa a wannan yankin, to za tasha kashi ba ƙarami ba, in ji Jaridar Haaretz.
"Duk da cewa babu wani shiri mai girma na kai hari kan kasar Labanon, Firaminista Netanyahu na fuskantar matsin lamba daga abokan hamayyar siyasa saboda gwagwarmayar da Falasdinawa suke yi a yankunan da aka mamaye da kuma ayyukan jirage marasa matuka na Hizbullah, lamarin da ya sanya shi cikin mawuyacin hali."
Kafafen yada labaran Isra'ila sun ruwaito cewa Isra'ila ba ta neman mamaye kudancin Lebanon har zuwa kogin Litani, sai dai kawai tana son gudanar da wani takaitaccen aikin soji a kan iyakar kasar domin tabbatar wa mazauna arewacin kasar cewa yankin na da amincin da zasu iya komawa domin cigaba da zama.
Jaridar ta Haaretz ta yi gargadi game da sarkakiyar al'amura a yankin, tana mai cewa irin wannan aiki, duk karancin shi na iya yamutsa yankin, har yakai ga lamarin ankasa shawo kanshi.
Martanin da kungiyar Hizbullah keyi kan hare haren sojin Isra'ila, na iya mayar da wannan dan karamin yunkuri na soji zuwa yaki na bai daya, kuma akwai yiyuwar kungiyar Hizbullah za ta kai hari kan gine-ginen manyan tsare-tsare na Isra'ila har ma da katsewar wutar lantarki.
Tun bayan kaddamar da Harin Guguwar Al-Aqsa a zirin Gaza, kungiyar Hizbullah ta fara kai hare-hare akai-akai a arewacin Palastinu da ta mamaye domin kare al'ummar Gaza.
