Wani tsohon jami'in Haramtacciyar Kasar Isra'ila ya ce kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon tana daya daga cikin Karfafa biyar dangane da adadin rokokin da ta mallaka, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.
Cibiyar labarai ta Al Mayadeen ta Beirut, ta nakalto tsohon mai ba shugaban ma'aikatan Isra'ila shawara kan tattalin arziki Ram Aminach a ranar Asabar yana cewa, "Al'ummar Isra'ila ba su fahimci girman barazanar Hizbullah ba," saboda tana da tarin rokoki, in ji shi.
Hezbollah tana daya daga cikin karfafa biyar, tare da Amurka, China, Rasha da Jamus, in ji shi.
Aminach ya bayyana cewa, Isra'ila ba za ta iya fuskantar kungiyar Hizbullah kaɗai ba, ba tare da fuskantar gaba dayan kasar Lebanon ba.
Jaridar Yedioth Aharonot ta Isra'ila ta bayyana cewa, kungiyar Hizbullah ta Lebanon tana da kayan yaki da fasahohi masu hatsarin gaske.
Rahoton ya ce gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na fuskantar makiya da ke da karfin soji da kuma mallakar makamai da fasahohi masu hadari kamar makamai masu linzami da jirage marasa matuka.
