Fasahar Zamani ta Sojojin Hezbollah Tana da Matukar Hadari inji wata Jaridar HKI

 


Jaridar Yedioth Aharonot ta Isra'ila ta bayyana cewa, kungiyar Hizbullah ta Lebanon tana da kayan yaƙi da fasahohi masu hatsarin gaske.


Rahoton ya ce gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na fuskantar makiya da ke da karfin soji sannan kuma suka mallaki kayyayaki da fasahohi masu hadari kamar makamai masu linzami da jirage marasa matuka.


Jaridar ta kara da cewa kutsawar daruruwan jirage marasa matuka daga kan iyakokin kasar Labanon ya nuna cewa jami'an tsaro da na soji ba su shirya fuskantar wadannan Jiragen marasa Matuƙa ba.


Jaridar ta rubuta cewa sojojin Isra'ila na matukar neman mafita daga barazanar kungiyar Hizbullah.


Tun bayan kaddamar da Guguwar Al-Aqsa a zirin Gaza, kungiyar Hizbullah ta fara kai hare-hare akai-akai a arewacin Palastinu da aka mamaye domin kare al'ummar Gaza.


Sakamakon hare-haren da dakarun Hizbullah ke kai wa, an kwashe akasarin mazaunan da ke arewacin Falasdinu da aka mamaye.


Kwanan nan, wani jirgin sama mara matuki na Hezbollah ya shiga arewacin Falasdinu da ta mamaye, ya kuma yi nasarar daukar hotunan muhimman sansanoni a tashar jiragen ruwa na Haifa, wanda kuma ya tabbatar da karfin 'Yan gwagwarmayar.


Muna roqon Allah daya cigaba da ba 'Yan Gwagwarmayar Musulunci Nasara akan Fajirai maqiya Allah.

Post a Comment

Previous Post Next Post