Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Saree ya sanar da cewa nan ba da dadewa ba za su kaddamar da wani sabon jirgin ruwa na soja da aka kera da fasahar zamani da kuma Karfin Lalatawa.
A cewar kafar yada labaran kasar Yemen Al-Masirah, Saree ya bayyana hakan ne a daren ranar Asabar.
Bai bayar da cikakken bayani game da jirgin na soja da kuma lokacin kaddamar da shi ba, amma ya ce kafafen yada labarai na yakin sojojin za su fitar da hotunan jirgin da tsakar ranar Lahadi.
A cewar kakakin, jirgin ruwan iri daya ne da wanda sojojin Yemen suka yi amfani da shi kusan mako guda da ya gabata wajen kai hari kan jirgin ruwa na Transworld Navigator a cikin tekun Bahar Maliya.
Tun a tsakiyar watan Nuwamba ne kasar Yemen ke kai hare-hare kan jiragen ruwa na Isra'ila ko kuma duk wani jirgin ruwa da ke kan hanyar zuwa tashar jiragen ruwa na yankunan Falasdinu da aka mamaye domin nuna goyon baya ga al'ummar Palasdinu dake Gaza. Kasar Yemen ta ce za a ci gaba da kai hare-haren har sai gwamnatin Isra'ila ta dakatar da yakin da take yi a zirin Gaza tare da janye shingen da ta yi wa yankin.
