A wani mataki na ba-zata, kungiyar kasashen Larabawa (Arab League) ta sauya matakin da ta dauka a shekarar 2016 na bayyana kungiyar Hizbullah a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, lamarin da ya share fagen kulla huldar diplomasiyya da kungiyar ta Lebanon.
A cewar mataimakin babban sakataren kungiyar Hossam Zaki, mambobin kungiyar sun amince da daina kiran kungiyar Hizbullah a matsayin kungiyar ta'addanci, saboda matakin da kungiyar ta dauka a baya-bayan nan kan HKI.
Matakin dai na nuni da wani gagarumin sauyi na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa kan kungiyar Hizbullah, wadda ta kasance babbar jigo a siyasar kasar ta Lebanon, kuma tana da matukar muhimmanci wajen adawa da mamayar Isra'ila.
Cire kungiyar Hizbullah daga jerin sunayen 'yan ta'adda na iya haifar da kara yunkurin diflomasiyya na yin cudanya da kungiyar, wanda zai iya sauya yanayin siyasa a Gabas ta Tsakiya.
