Ƙasar Spain ta mika buƙatar ta na shiga ƙarar da Afirka ta Kudu ta shigar kan Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila a Kotun Duniya (ICJ).
Tashar talabijin ta Aljazeera ta nakalto Ministan Harkokin wajen Spain Jose Manuel Albares yana fadar haka a yau Asabar inda yake cewa: "Mun yanke wannan shawarar ne bisa la'akari da ci gaba da aikin soji a Gaza."
"Mun kuma damu matuƙa game da tsawaita rikicin yankin," in ji shi. "Manufarmu tilo ita ce kawo karshen yakin da kuma ci gaba a kan hanyar aiwatar da yarjejeniyar kasashen biyu."
A ranar 6 ga watan Yuni, Albares ya yi kira da a shiga tsakani a shari'ar Afirka ta Kudu kan gwamnatin HKI a kotun ICJ, yana zargin gwamnatin da kisan kare dangi a Gaza.
Spain ta shiga cikin rukunin ƙasashe ciki har da Ireland waɗanda suka nuna sha'awar shiga cikin lamarin. Yayin da Kasashen Ireland, Spain da Norway kwanan nan suka amince da kasar Falasdinu.
Ministan na Spain ya ce Madrid na son tallafa wa kotun ta ICJ wajen aiwatar da duk wasu matakan da ta umarta, kamar umarnin gwamnatin kasar na dakatar da ayyukan soji a birnin Rafah da ke kudancin Gaza.
Albares ya sanar da cewa Spain na yin hakan ne saboda jajircewarta ga dokokin kasa da kasa, da sha'awar tallafawa ayyukan kotun, da kuma karfafa Majalisar Dinkin Duniya ta hanyar mara wa ICJ baya a matsayin babbar hukumar shari'a a tsarin.
Kotun ta ICJ ita ce babbar hukumar shari'a ta Majalisar Dinkin Duniya, wadda aka kafa a shekara ta 1945 don warware takaddama tsakanin jihohi.
