A ranar Juma'a 28 ga watan Yunin 2024 ne kungiyar Hezbullah ta kaddamar da hare-hare kan yankunan Isra'ila, domin nuna goyon baya ga al'ummar Palasdinu a zirin Gaza da kuma daukar fansa kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa kauyukan kudancin kasar da gidajen fararen hula.
Da misalin karfe 3:42 na rana, mayakan na Islama sun kai hari kan wani taron sojojin Isra'ila da ke kusa da yankin Al-Tayhat mai ratsawa ta hanyoyi uku da makaman roka, inda suka kai harin kai tsaye. Wannan harin ankai shine domin goyon bayan al'ummar Palasdinu.
Haka zalika kuma, mayakan na Islama sun kai hari kan wani gini da sojojin Isra'ila ke amfani da shi a matsugunin "Shlomi", inda suka kai hari kai tsaye. Wannan harin na ramuwar gayya ne kan harin da Isra'ila ta kai kan kauyukan kudancin kasar da gidajen fararen hula, musamman a kauyen Chihine.
Karfe 8:00 da kuma 8:05 na dare, mayakan Islama sun kai hari a Ruwaiset Al-Qarn da kuma Al-Summaqa da ke gonakin Shebaa da tsaunin Kfarchouba da aka mamaye, da makaman roka, inda suka kai hare haren kai tsaye a dukkan guraren biyu.
A wani hari na karshe da kungiyar Musulunci ta Hezbullah ta kai, ta yi amfani da wasu gungun jirage marasa matuka wajen kai hari kan hedikwatar bataliya ta 411 da ke "Ga'aton", inda suka kashe tare da jikkata wasu jami'ai da sojojin Isra'ila. Anyi Nasarar Harin lamarin daya haddasa Tashin wuta a yankin.
"Kuma nasara ba ta kasance ba face daga Allah, Mabuwayi, Mai hikima."
