Jerin Hare Haren da Kungiyar Hezbullah Takai a Ranar 27 ga Watan Yuni, 2024

 


Jaridar Al-Ahed Mallakin Ƙungiyar Hezbullah ta rawaito cewa: Kungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta kaddamar da hare-hare a kan yankunan Isra'ila a ranar 27 ga watan Yunin 2024.


 Hare-haren sun hada da wani samame da aka kai ta sama da jiragen sama marasa matuka a tashar jiragen ruwa na Naqoura, inda suka auna jami'ai da sojojin Isra'ila.


Har ila yau, mayakan na musulunci sun kai hari kan Ruwaiset Al-Qarn da ke gonakin Shebaa da suka mamaye da makaman roka, inda suka kai musu hari kai tsaye. Bugu da kari, sun yi ruwan bama-bamai a babban sansanin tsaron Sojin sama da Sojin makami mai linzami na rundunar Arewa da ke barikin "Birya" da Rokokin Katyusha masu yawa.


An kai hare-haren ne domin nuna goyon baya ga al'ummar Palasdinu a zirin Gaza da kuma ramuwar gayya kan harin da Isra'ila ta kai kan Nabatieh da Sohmor. Kungiyar gwagwarmayar Musuluncin ta bayyana cewa "Nasara tana zuwa ne kawai daga Allah, Mabuwayi, Mai hikima".

Post a Comment

Previous Post Next Post