Shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hasan Nasrallah ya yabawa Iran akan tsayin dakanta gurin rashin saurarawa Azzalumai da 'yan mulkin mallaka, a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin daga birnin Beirut.
Sayyid Nasrallah ya yi jawabi a yayin bikin tunawa da cika kwanaki 40 da Shahadar Shugaba Ibrahim Raeisi da Muƙarraban sa a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu, ta hanyar kafar bidiyo. Inda ya bayyana Iran a matsayin abin koyi gurin tsaurarawa ga Azzalumai da 'yan mulkin mallaka.
Sayyid Nasrallah ya yi tsokaci kan matakin da Iran ta dauka kan kisan da aka yi wa manyan kwamandojin soji da suka hada da Qassem Soleimani da Abu Mahdi al-Muhandis, lamarin da ya ce ya mayar da barazana zuwa wata dama. Ya yaba da harin makami mai linzami da Iran ta kai kan sansanonin Amurka a Iraki da kuma harin da ta kai kai tsaye kan Isra'ila a cikin watan Afrilu, wanda ya sa Isra'ila ta kadu matuka.
Sayyid Nasrallah ya ce wannan mummunan rashi na shugaba Raeisi da abokan Tafiyarsa misali ne na karfi da hadin kan Iran. Ya yabawa miliyoyin mutanen da suka fito kan tituna a biranen Iran, yana mai cewa fitowar tasu tana dauke da sako mai karfi ga abokai da makiya.
Sayyid Nasrallah ya kammala da cewa tsarin mulkin ƙasar Iran mai tsarki ba wai kawai na al'ummar Iran kaɗai bane, shi tsarin shine makomar kasashe da gwamnatocin yankin. Ya kuma yaba da gaskiya, tare da bayyana gaskiya da kuma nuna gaskiya a cikin ayyukanta, yana mai cewa ta zama abin koyi ga yunkurin gwagwarmaya a yankin baki daya.
