Daga Fara Yaƙin Gaza Zuwa Yanzu Amurka Ta Ba da Tallafin Dala Biliyan 6.5 ga ‘Isra’ila

 


 An bayar da rahoton cewa, Amurka ta ba da taimakon tsaro na Dala Biliyan 6.5 ga "Isra'ila" tun bayan da 'yan mamayar suka kaddamar da yakinsu na kisan kare dangi a zirin Gaza.


Jaridar Washington ta rawaito wani babban jami'in gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden da ba a bayyana sunansa ba a ranar Larabar da ta gabata cewa kusan rabin kudaden an bayar da su ne a watan da ya gabata kadai.


 "Wannan wani gagarumin aiki ne mai girma," in ji jami'in, ya kara da cewa an bayyana adadin ne yayin tattaunawa tsakanin manyan jami'an fadar White House da ministan harkokin soji na 'Isra'ila' Yoav Gallant a Washington a wannan mako.


Rahoton ya ce jami’in na Amurka ya bayyana adadin “a matsayin manuniya mai zurfi da sarkakiyar tallafin da Amurka ke ba ‘Isra’ila’.


 Ya kuma kara da cewa, furucin ya sabawa ikirari da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi na cewa Washington ɗin ta daina bada tallafin Makamai.


A cikin wani faifan bidiyo da aka ɗaura a manhajar X ranar Talata, Netanyahu ya yi zargin cewa gwamnatin Biden tana "riqe" makamai da alburusai zuwa Tel Aviv.


 Taimakon sojan Amurka ga "Isra'ila", gami da samar da muggan makamai na biliyoyin daloli, shine jigo gurin taimakon kisan kare dangin Falasdinawa da ake yi a Gaza sannan kuma yana taimakawa gurin tsawaita mummunan yakin matuka.


 Amurka ta kasance babbar kawar Isra'ila kuma babbar mai samar da makamai. Yayin da take baiwa "Isra'ila" tallafin makamai da bayanan sirri a lokacin yakin Gaza, tare da toshe kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da ke neman tsagaita bude wuta a yankin Falasdinu da akayi wa kawanya.

Post a Comment

Previous Post Next Post