Kungiyar Islamic Jihad ta Yabawa 'Yan Gwagwarmayar Falasdinawa a Sansanin Jenin

 


Kungiyar Islamic Jihad ta Falasdinu ta yaba da farmakin baya-bayan nan da dakarun gwagwarmayar Falasdinawa suka kai a sansanin Jenin da ke gabar yammacin kogin Jordan, wanda ya yi sanadin mutuwar sojan Isra'ila daya tare da jikkata wasu 16.


A cewar kungiyar, an kaddamar da wannan farmakin ne domin mayar da martani ga ayyukan da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da yi a yankin yammacin kogin Jordan da zirin Gaza, lamarin dake janyo hasarar rayuka da wahala a tsakanin al'ummar Falasɗinu.


 Kungiyar Islamic Jihad ta yaba da wannan farmakin a matsayin nuni da irin yadda al'ummar Palastinu suke da himma wajen tunkarar yankunansu da kuma azamar tunkarar wannan mummunan yakin ta'addanci da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kaddamarwa, wanda Amurka ke marawa baya.


Wannan farmakin dai shi ne na baya bayan nan a jerin gwabzawar da ake yi tsakanin dakarun gwagwarmayar Palasdinawa da sojojin Isra'ila, lamarin da ya kara tada zaune tsaye a yankin.


 A cewar ma'aikatar lafiya ta Gaza, sama da Falasdinawa 37,590 ne aka kashe tare da jikkata 86,032 a ci gaba da kisan kiyashin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar data Gabata.

Post a Comment

Previous Post Next Post