Wani babban masani kan alakar kasa da kasa ta kasar Labanon ya bayyana cewa, Alhuda Hudan Hizbullah yayi buji buji da taqamar sojojin Isra'ila tare da lalata tatsuniyar karfin wannan sojojin.
Yayin da yake ishara da ayyukan leken asirin da kungiyar Hizbullah ta yi a baya-bayan nan kan gwamnatin sahyoniyawan, Adnan Allameh ya yi nuni da cewa, ayyukan leken asiri na kungiyar gwagwarmayar na daya daga cikin mafi zafi tun bayan kafa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Ya kara da cewa makiya sun kadu da wannan aiki ta yadda ba su da wata hujja ta gazawar wannan leken asirin, a lokaci guda kuma anyi nasara akan dukkanin na'urorin tsaro, in ji shi.
Ya ce idan aka yi la'akari da cewa matsugunan Isra'ila sun fuskanci rashin tsaro a cikin 'yan watannin da suka gabata, tare da raba dubun-dubatarsu daga matsugunansu. Wannan aiki zai rubanya yanayin rashin tsaro a tsakanin 'yan Isra'ilan mazauna yankunan Falasdinawa da aka mamaye tsawon shekaru da dama, in ji shi.
Allameh ya ci gaba da cewa, wannan Aikin da akayi wani mataki ne na gazawa wajen leken asiri tare da yin barazana ga tsaron gwamnatin sahyoniyawan, inda wani karamin jirgi mara matuki ya samu nasarar shawo kan tsarin tsaro mafi ci gaba da kuma daukar sahihan hotuna na muhimman abubuwan da makiya suke da shi.
Ya ce tuni dakarun (na Hezbullah) suka gano inda za su iya kaiwa hari kuma suna da makaman da za su kai musu hari.
Isra'ilawan sun san cewa 'Yan Gwagwarmayar na iya kai hari a duk yankunan da aka mamaye, sannan kuma idan sukayi kuskuran kai hari Labanon, duk yankunan nan za'a tarwatsa su.
