Hezbollah ta kai Hari kan Sansanin Al-Motellah na HKI

 


Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta ce ta kai hari kan sansanin al-Motellah na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da ke arewacin kasar Falasdinu da Aka Mamaye.


 Kamfanin dillancin labaran Samaa dake Falasdinu ya bayar da rahoton cewa, makami mai linzami na kungiyar Hizbullah ya lalata wata motar sojin Isra'ila, inda ya kashe ko jikkata dukkan sojojin da ke ciki.


Kafofin yada labaran gwamnatin sahyoniyawan sun kuma tabbatar da harin yayin da suke bayar da rahoton faruwar wani lamari mai sarkakiya da hatsarin gaske a yankin na Motellah.


 Kafofin yada labaran sun ruwaito cewa sojojin Isra'ila 5 sun samu munanan raunuka.


 Harin Hezbollah kan al-Motellah ya faru ne a lokacin da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ke magana a wani taron manema labarai.


A wani labarin kuma, gidan Talabijin na Al Mayadeen sun bayar da rahoton cewa, jiragen yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a birnin Khiam da ke kudancin kasar Labanon.


Tashar talabijin din ta ce ba a samu rahoton asarar rayuka ba tukuna.


 Rahotanni sun ce an kai harin ne bayan da kungiyar Hizbullah ta kaddamar da harin makami mai linzami kan sansanin sojin gwamnatin sahyoniyawan.


Kungiyoyin gwagwarmaya na yankin da suka hada da Hezbollah da kungiyar gwagwarmayar Musulunci a Iraki da kuma Ansarullah ta Yaman sun bayyana cewa za su ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin sojin Isra'ila domin nuna Goyon Bayan Falasdinawa da ake wa kisan kare dangi tun watan Oktoban shekarar data gabata.

Post a Comment

Previous Post Next Post