A 'yan makonnin da suka gabata gwamnatin Isra'ila ta yi barazanar Afkawa kasar Lebanon da wani gagarumin yaki yayin da ake ci gaba da gwabza fada da kungiyar Hizbullah. Sai dai duk da wannan barazanar, rahotanni sun nuna cewa lamura na Ƙara dagulewa a cikin bangarorin siyasa da na sojin Isra'ila tare da gargadin cewa wannan yaƙin zai haifar da Babbar barna, wadda zata haɗa harda Birnin Haifa mai tashar jiragen ruwa.
A cewar rahoton ranar Lahadi da jaridar Al Akhbar ta kasar Labanon ta fitar, barazanar da Isra'ila ke yi na fadada yakin da take yi da kasar Labanon ya bar baya da kura, yayin da damuwa da fargaba ke kara ta'azzara a cikin harkokin siyasa da kafafen yada labarai da ma sojojin Isra'ilan, inda suka bayyana yaƙin a matsayin kisan kai ga Isra'ila.
Shugabannin sojojin Isra'ila sun damu matuka cewa sojojinsu ba su da karfin fada a fagage da dama a lokaci guda, kuma yaƙi da Hizbullah zai iya haifar da bala'i da halaka a Isra'ila.
Wani farfesa a jami'ar Haifa ya yi gargadin cewa yaki da kungiyar Hizbullah zai iya lalata kashi uku na gidajen da ke Haifa tare da lalata birnin daga dubban makamai masu linzami.
Wani tsohon kwamandan tsaron saman Isra'ila, Zvika Haimovich, ya damu da karfin makamai masu linzami na Hezbollah da kuma Jiragen su maras matuka, wanda ya ce sojojin dake gaba dasu akan hakan a duniya basu da yawa.
Kungiyar Hizbullah ta zama runduna mai karfi da ci gaba mai dauke da makamai da fasahar kere-kere, wanda hakan ya zama babbar barazana ga sojojin Isra'ila da kayayyakin more rayuwa, a cewar jaridar Haaretz.
Jiragen yaki marasa matuka na Hezbollah sun taimaka wa kungiyar sosai, lamarin da ya basu damar kalubalantar Isra'ila, a cewar Haaretz. Jaridar ta yi imanin cewa, Hezbollah ta shirya tsaf domin yaki mai tsayi, da neman durkusar da Isra'ila ta hanyar wannan yaƙin.
Muna Rokon Allah daya ba 'Yan Gwagwarmayar Musulunci Nasara Akan Makiya Allah.
