Yemen Takai Hari kan Jirgin Ruwan USS Eisenhower da Makamai Masu Linzami

 


Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Saree ya bayyana cewa, dakarun kasar sun kai wani hari da makamai masu linzami kan wani jirgin ruwan Amurka Eisenhower dake Dakon Jiragen yaƙi a tekun Bahar Maliya.


 A cikin wata sanarwa a Jiya Asabar, mai magana da yawun ya ce an kai harin ne “kai tsaye” da makamai masu linzami da dama.


A wani farmakin da ba a taba yin irinsa ba, sojojin ruwan Yamen sun kuma kai hari kan jirgin ruwa na Transworld Navigator a cikin Tekun Arabiya da makamai masu linzami da dama, in ji Saree.


 Ya kara da cewa, an yi nasarar dukkan hare haren biyu, inda aka kai harin kai tsaye kuma akayi nasara.   


 Kakakin ya jaddada cewa dakarun kasar Yemen za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na soji domin tallafawa al'ummar Palastinu har sai gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta daina kai hare-hare a zirin Gaza.


Ya kara da cewa, dakarun kasar Yemen ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kai farmaki kan sojojin kasashen waje masu adawa dasu a Tekun Bahar Maliya da Tekun Larabawa, domin mayar da martani ga hare-haren da ake kai wa kasar Yemen.


 Kasar ta Larabawa dai, tun daga tsakiyar watan Nuwamba, ta fara kai hare-hare kan jiragen ruwan Isra'ila da kuma Jiragen ruwan da suke kan hanyar zuwa tashar jiragen ruwa a yankunan Falasdinawa da ta mamaye, a matsayin martani ga yakin Gaza.


Kasar Yemen na ci gaba da kai hare-haren soji kan jiragen ruwan da ke da alaka da Isra'ila a cikin teku duk da hare-haren hadin gwiwa da Amurka da Birtaniya suke kaiwa kan kasar Yemen tun a tsakiyar watan Janairu. 


 Kasar Yemen ɗin ta ce hare-haren da ake kai mata ta sama na da nufin baiwa gwamnatin Isra'ila karin goyon baya ne kawai.

Post a Comment

Previous Post Next Post