Kasuwanci Tsakanin Iran da Turkiyya Ya kai Darajar Dala Biliyan 2.3 a Cikin Watanni 5

 


Cibiyar kididdiga ta Turkiyya (TURKSTAT) ta bayyana jimillar kimar ciniki tsakanin Iran da Turkiyya a cikin watanni biyar na farkon shekarar 2024 Yakai Dala Biliyan 2.3.


Bisa kididdigar da aka yi, an yi musayar kayayyaki da darajarsu ya kai dalar Amurka biliyan 2.3 tsakanin Iran da Turkiya daga watan Janairu zuwa Mayun shekarar 2024, wanda ya nuna karuwar kashi 5% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata (Daga Janairu zuwa Mayun shekarar 2023).


Kasashen biyu sun yi musayar kayayyakin da ba na mai ba (Non Oil) na dalar Amurka biliyan 2.189 daga watan Janairu zuwa Mayun 2023.


Bisa wannan rahoto, kayayyakin da Turkiyya ta fitar sun zarce dala biliyan 1.340, wanda ya nuna karuwar kashi 16% idan aka kwatanta da na bara.


Turkiyya ta shigo da kayayyakin da darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 960 daga Iran a cikin watanni biyar zuwa watan Mayu.


Kayayyakin da ba mai ba (Non-oil) da Turkiyya ta shigo da su daga Iran ya kai dala biliyan 1.038 daga watan Janairu zuwa Mayun 2023.

Post a Comment

Previous Post Next Post