Kafofin yada labaran yahudawan sahyoniya sun sanar cewa kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka a kan matsugunan HKI a arewacin Falasdinu da ta mamaye tare da halaka 130 daga cikinsu.
Wasu gine-gine da cibiyoyin samar da ababen more rayuwa 1,023 ne jiragen yaki marasa Matuƙa da makamai masu linzami na Hezbullah suka kaima hari a yankunan da aka mamaye, kamar yadda kafafen yada labaran yahudawan sahyuniya suka tabbatar a yau Talata.
Al Mayadeen ta ruwaito cewa yaƙin ɗauki ɗai ɗai da ake yi da ‘yan mamayar a arewacin yankunan da aka mamaye ya kai ga halaka fiye da matsugunai 130.
Makonni kadan da suka gabata ma'aikatar tsaron Isra'ila ta amince da tasirin hare-haren da mayakan Hizbullah suka kai kan sansanonin sojin yahudawan sahyoniya da matsugunan arewacin Gaza da suka mamaye.
A cikin sanarwar da ta fitar, ma'aikatar Isra'ila ta ce 130 daga cikin 155 na gidajen yahudawan sahyoniya dake Kibbutz Manara sun lalace sakamakon hare-haren makamai masu linzami na Hezbollah.
Ta kara da cewa gidaje 124 na Qiryat Shemona sun kuma lalace yayin rikicin da kungiyar Hizbullah ta Lebanon.
Kwanan nan, kafofin yada labaran yahudawan sahyuniya sun ba da rahoton cewa, 'yan gwagwarmayan na Lebanon sun harba makamai masu linzami sama da 3,000 kan yankunan Falasdinawa da aka mamaye domin kai hari kan sansanonin sojojin Isra'ila tun farkon yakin Gaza a watan Oktoban 2023.
Kungiyar Hizbullah ta sha sanar da cewa tana kai hare-haren nata ne domin goyon bayan Falasdinawa da ake zalunta, da nufin tilastawa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila dakatar da kai hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar Gaza inda aka kashe kusan mutane 38,000 galibi mata da kananan yara a zirin Gaza.
