Dakarun Al-Qassam, reshen soji na kungiyar Hamas, sun kai hare-hare kan wurare da kayan aikin soji mallakin rundunar tsaron HKI. A wani lamari na baya-bayan nan, sun kai hari kan kayan aikin soji daban-daban, ciki har da tankar Merkava IV.
A cewar kafar yada labaran Falasdinu, Dakarun Al-Qassam sun sanar a ranar Talata cewa, sun kai hari kan tankar Merkava IV ta Isra'ila da makamin roka Yassin 105 a unguwar Al-Shajaiyeh da ke gabashin birnin Gaza.
Har ila yau, reshen sojin kungiyar Hamas sun sanar cewa mayakan na su sun kai hari kan wasu gungun sojojin sahyoniyawan su 14 inda suka yi musu kwanton ɓauna a wani gida a Al-Shuja'iyya da Makamin TBG tare da kashe su ko kuma jikkata su.
Dakarun na al-Qassam sun kai hari kan wata Mota mai Sulke ta sojin HKI da aka fi sani da ‘Tiger’ a yankin Al-Shuja’iyya ta hanyar amfani da makamin roka 105.
