Dr. Masoud Pezeshkian ne ya lashe zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka gudanar a Jiya Juma'a inda ya zama shugaban kasar Iran na 9.
Daga cikin jimillar kuri'u 30,530,157 da aka kirga, Pezeshkian, ya samu kuri'u 16,384,403 yayin da Jalili ya tsaya bayan abokin takararsa da kuri'u 13,538,179. An bayar da rahoton cewa cikin kashi 100% na mutanen da suka cancanci kaɗa ƙuri'a a ƙasar an samu fitowar kashi 49.8%.
Pezeshkian mai shekaru 69, ya taba zama dan majalisa a majalisar dokokin Iran tsawon shekaru 5.
Ya kuma kasance mataimakin kakakin majalisar dokokin Iran ta 10. Zababben shugaban ya rike mukamin ministan lafiya na Iran na tsawon shekaru hudu a lokacin gwamnatin shugaba Muhammad Khatami.
A ranar 28 ga watan Yuni ne aka gudanar da zaben farko a duk fadin kasar Iran tare da halartar 'yan takara hudu.
Masoud Pezeshkian da Saeed Jalili sun samu kuri'u fiye da sauran 'yan takarar, saboda haka aka shirya gudanar da zaben fidda gwani karo na biyu a mako mai zuwa saboda babu daya daga cikin 'yan takarar da ya samu nasarar samun rinjayen kuri'u domin ya zama shugaban kasar Iran."
A dokar Iran dole Ɗan takara ya zama ya samu fiye da kaso 50% na ƙuri'u da aka Jefa kafin ya zama shugaban ƙasar Iran.
Bisa alkaluman da aka bayar, Masoud Pezeshkian ya samu nasara da kuri'u 16,384,403 daga cikin jimillar kuri'u 30,530,157 da aka kirga.
Don lissafin kason da ya samu, zamu iya raba adadin kuri'un da ya ci (16,384,403) da jimillar kuri'un da aka kirga gaba daya (30,530,157), sannan mu ninka da 100:
(16,384,403 ÷ 30,530,157) x 100 = 53.6%
Don haka Masoud Pezeshkian ya lashe zaben shugaban kasar Iran da kashi 53.6% na kuri'un da aka kada.
