Jaridar Isra'ila Hayom ta Sahayoniya ta buga wani rahoto a yau Lahadi inda ta yi bayani dalla-dalla akan abinda hukumomin tsaro suka fitar, wanda ke bayyana kalubalen da Mazaunan HKI za su iya fuskanta a yayin Yaƙi da kungiyar Hizbullah ta Lebanon.
Jaridar Isra'ila Hayom ta rawaito cewa Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta fitarwa jami'anta da ke arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye abubuwan da zasu iya faruwa yayin gagarumin yaki da kungiyar Hizbullah.
A cewar umarnin, a yayin da ake gwabza kazamin yaki da kungiyar Hizbullah, ana sa ran za a samu katsewar wutar lantarki na akalla sa'o'i 72, tare da kawo cikas ga ayyukan intanet da na wayar tarho na tsawon sa'o'i 24-48.
Bugu da ƙari, na'urorin sanarwa, da suka hada da sanarwar wayar hannu, za a katse su, saboda haka za a sanar dasu ta hanyar sanarwar lasifikar gargajiya.
Haka zalika za'a samu katsewar ruwa na akalla mako guda a manyan yankunan Falasdinu da aka mamaye sakamakon yakin da gwamnatin kasar zata yi da kungiyar Hizbullah.
Umurnin ya umurci mazauna, har ma da mazauna Tel Aviv, da su kasance a gidajen su na akalla kwanaki uku.
A bisa wannan umarni, akwai yiwuwar tabarbarewar samar da abinci da rarraba kayan abinci, da karuwar ayyuka a asibitoci, da yawaitar gudun hijira daga arewaci da tsakiya zuwa kudancin Palasdinu da ta mamaye, wadannan su ne sauran sakamakon da yaƙi da kungiyar Hezbullah zai iya haifarwa.
