Zaɓaɓɓen Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Goyon Bayan sa Ga Kungiyoyin Gwagwarmaya

 


A cikin sakon da ya aika wa Sayyid Nasrallah, zababben shugaban kasar Iran ya sha Alwashin goyon bayan 'Yan Gwagwarmayan.


 Zababben shugaban kasar Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa goyon bayan da Iran ke ba wa Dakarun Musulunci zaya ci gaba a wa'adin mulkinsa.


Dangane da sakon taya murna da babban sakataren kungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah ya aike a yau litinin, zababben shugaban kasar Masoud Pezeshkian ya sha alwashin cewa kungiyoyin gwagwarmaya ba za su bari haramtacciyar gwamnatin Isra'ila ta ci gaba da aiwatar da manufofinta na aikata laifuka ba.


Zababben shugaban kasar Iran ya tabbatar da cewa Iran tana goyon bayan kungiyoyin gwagwarmayar yankin da suke adawa da haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawa, wadanda suka samo asali daga manufofinmu masu tsari, da gadon marigayi Imam Khumaini, da kuma jagorancin Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.


Pezeshkian ya kara da cewa, "Ina da yakinin cewa kungiyoyin gwagwarmaya na yankin ba za su bari Gwamnatin HKI ta ci gaba da aiwatar da manufofinta na yaƙin ta'addanci a kan al'ummar Palastinu da sauran kasashen yankin da ake zalunta ba."


Pezeshkian ya yi fatan nasara da wadata ga Nasrallah da al'ummar Labanon, da kuma nasarar Ubangiji ga jaruman gwagwarmaya.

Post a Comment

Previous Post Next Post