Shugaban kungiyar Ansarullah ya ce Isra'ila ba za ta iya Jurewa Hare-haren da Ake kai wa a Tekun Bahar Maliya ba

 


Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyed Abdul-Malik Al-Houthi, ya bayyana a wani jawabi da ya yi a gidan talabijin cewa, kasar Yemen za ta ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa da ke zuwa Isra'ila a Tekun Bahar Maliya, yana bayyana wannan matsayi a matsayin wanda ba za a iya jurewa ba kuma babban tushen matsin lamba ga sahyoniyawan


Sayyed Al-Houthi ya ce, “Wannan matsaya ta harzuka makiya matuƙa ta yadda ba zasu iya jure mata ba. Kuma hakan ya zama babbar matsala sannan kuma tushen matsin lamba babba ga sahyoniyawan.


Ya jaddada cewa Amurka, Birtaniya, da kuma "Isra'ilawa" sun keta 'yancin Yemen, yayin da suke yin rikici kai tsaye da ƙasar.


Har ila yau ya bayyana cewa zaluncin da ake yi wa al'ummar kasar Yamen cin zarafi ne a fili, wanda ya zama wani mataki na wuce gona da iri kan al'ummar kasar Yemen baki daya.


Sayyed Al-Houthi ya yi wa Amurka izgili da cewa suna kiran wasu ‘yan ta’adda, yana mai cewa Amurka dai itace ke goyon bayan laifukan da Isra’ila ke yi, saboda haka ba ta da wata hujjar da za ta hukunta wasu. Ya kuma ce matakin na Amurka ba zai tsorata ko raunana al'ummar Yemen ba.


Ya nuna Amurka a matsayin abin ban mamaki yayin take kiran wasu ‘yan ta’adda bayan ta kai musu hari tsawon shekaru 9.


Sayyed Al-Houthi ya tabbatar da cewa tushen aikata laifuka, ta'addanci, da mulkin kama karya, ita ce Amurka, wacce ba ta da cancantar yanke hukunci kan wasu.


Ba tare da bata lokaci ba, ya ce, "Za mu dage wajen kai hari kan jiragen ruwa masu alaka da 'Isra'ila' da kuma harba makamai masu linzami zuwa yankunan Falasdinu da ta mamaye har sai an kawo karshen hare-hare da kuma mamaye Gaza."


Tun a farkon watan Oktoba, Amurka da kawayenta na Yamma suke goyon bayan yakin soji na "Isra'ila", wanda aka kira da yaƙin kare dangi.


Sojojin Yaman da kungiyar Ansarullah sun kai hari kan jiragen ruwan Isra'ila a tekun Bahar Maliya domin tallafa wa Falasdinawa. Sayyed Al-Houthi ya yi kira da a gudanar da gagarumar zanga-zanga a yau Juma'a, ya kuma bukaci 'yan kasar Yemen a ko'ina da su shiga cikin wannan zanga-zangar, ya kuma bukaci 'yan Yemen da ke Amurka da Turai da suma su yi zanga-zanga kamar na Yemen. Ya kuma yi kira ga Larabawa da musulmin duniya da su jagoranci zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinawa da kuma tsayawa tsayin daka don kare bil'adama.

Post a Comment

Previous Post Next Post